< Romawa 1 >

1 Bulus, bawan Kiristi Yesu, kirayaye don yă zama manzo, keɓaɓɓe kuma domin bisharar Allah.
Paul, a servant of Jesus Christ, a called apostle, having been separated to the good news of God —
2 Bisharar da Allah ya yi alkawari tuntuni ta bakin annabawansa a cikin Nassosi Masu Tsarki
which He announced before through His prophets in holy writings —
3 game da Ɗansa. Wanda bisa ga mutuntakarsa, zuriyar Dawuda ne.
concerning His Son, (who is come of the seed of David according to the flesh,
4 Wanda bisa ga Ruhun tsarki, an shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ne ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne.
who is marked out Son of God in power, according to the Spirit of sanctification, by the rising again from the dead, ) Jesus Christ our Lord;
5 Ta wurinsa da kuma saboda sunansa, muka sami alheri muka kuma zama manzanni don mu kira mutane daga cikin dukan Al’ummai zuwa ga biyayyar da take zuwa daga bangaskiya.
through whom we did receive grace and apostleship, for obedience of faith among all the nations, in behalf of his name;
6 Ku ma kuna cikin waɗanda aka kira ku zama na Yesu Kiristi.
among whom are also ye, the called of Jesus Christ;
7 Wannan wasiƙa ce zuwa ga dukanku da kuke a Roma waɗanda Allah yake ƙauna, waɗanda kuma ya kira domin su zama tsarkaka. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma daga Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
to all who are in Rome, beloved of God, called saints; Grace to you, and peace, from God our Father, and [from] the Lord Jesus Christ!
8 Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.
first, indeed, I thank my God through Jesus Christ for you all, that your faith is proclaimed in the whole world;
9 Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin wa’azin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku
for God is my witness, whom I serve in my spirit in the good news of His Son, how unceasingly I make mention of you,
10 cikin addu’o’ina a kowane lokaci; ina kuma addu’a cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za tă buɗe mini in zo wurinku.
always in my prayers beseeching, if by any means now at length I shall have a prosperous journey, by the will of God, to come unto you,
11 Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi
for I long to see you, that I may impart to you some spiritual gift, that ye may be established;
12 wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu.
and that is, that I may be comforted together among you, through the faith in one another, both yours and mine.
13 Ina so ku sani’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.
And I do not wish you to be ignorant, brethren, that many times I did purpose to come unto you — and was hindered till the present time — that some fruit I might have also among you, even as also among the other nations.
14 Ina da hakki ga Hellenawa da waɗanda ba Hellenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci.
Both to Greeks and to foreigners, both to wise and to thoughtless, I am a debtor,
15 Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku wa’azin bishara ku ma da kuke a Roma.
so, as much as in me is, I am ready also to you who [are] in Rome to proclaim good news,
16 Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai.
for I am not ashamed of the good news of the Christ, for it is the power of God to salvation to every one who is believing, both to Jew first, and to Greek.
17 Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
For the righteousness of God in it is revealed from faith to faith, according as it hath been written, 'And the righteous one by faith shall live,'
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu,
for revealed is the wrath of God from heaven upon all impiety and unrighteousness of men, holding down the truth in unrighteousness.
19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi.
Because that which is known of God is manifest among them, for God did manifest [it] to them,
20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja. (aïdios g126)
for the invisible things of Him from the creation of the world, by the things made being understood, are plainly seen, both His eternal power and Godhead — to their being inexcusable; (aïdios g126)
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.
because, having known God they did not glorify [Him] as God, nor gave thanks, but were made vain in their reasonings, and their unintelligent heart was darkened,
22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye,
professing to be wise, they were made fools,
23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.
and changed the glory of the incorruptible God into the likeness of an image of corruptible man, and of fowls, and of quadrupeds, and of reptiles.
24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya.
Wherefore also God did give them up, in the desires of their hearts, to uncleanness, to dishonour their bodies among themselves;
25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin. (aiōn g165)
who did change the truth of God into a falsehood, and did honour and serve the creature rather than the Creator, who is blessed to the ages. Amen. (aiōn g165)
26 Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba.
Because of this did God give them up to dishonourable affections, for even their females did change the natural use into that against nature;
27 Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
and in like manner also the males having left the natural use of the female, did burn in their longing toward one another; males with males working shame, and the recompense of their error that was fit, in themselves receiving.
28 Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba.
And, according as they did not approve of having God in knowledge, God gave them up to a disapproved mind, to do the things not seemly;
29 Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne,
having been filled with all unrighteousness, whoredom, wickedness, covetousness, malice; full of envy, murder, strife, deceit, evil dispositions; whisperers,
30 da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu;
evil-speakers, God-haters, insulting, proud, boasters, inventors of evil things, disobedient to parents,
31 su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi.
unintelligent, faithless, without natural affection, implacable, unmerciful;
32 Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.
who the righteous judgment of God having known — that those practising such things are worthy of death — not only do them, but also have delight with those practising them.

< Romawa 1 >