< Ru’uya ta Yohanna 9 >
1 Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. (Abyssos )
第五位天使吹响号角,我看着一颗星从天上掉到地上。这颗星被赋予了打开深渊的钥匙。 (Abyssos )
2 Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. (Abyssos )
他打开深渊,有烟从里面冒出来,就像一个巨大火炉飘出的烟,太阳和天空因这深渊的烟而变黑。 (Abyssos )
3 Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya.
有蝗虫从烟中爬到地上;他们被赐予如地面蝎子一般的力量。
4 Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani.
对他们的吩咐是,不可伤害地上的草和所有植物或树木,只可伤害那些额上没有上帝印记之人。
5 Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum.
蝗虫没有杀戮的能力,只是让他们像被蝎子螫了一样痛苦五个月。
6 Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu.
在那段时间,人们寻死却无法如愿;想要死亡,死亡却远离他们。
7 Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane.
蝗虫的样子就像一匹匹战马,头上戴的仿佛金冠冕,脸像人的面孔,
8 Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki.
头发好像女人的长发,牙齿好像狮子;
9 Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi.
它们的胸甲如铁甲,翅膀的声音好像许多车马飞驰上战场的声音。
10 Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar.
它们有着蝎子一样的尾巴和毒刺,尾巴对人的伤害能持续五个月。
11 Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon. (Abyssos )
它们的统治者是深渊的天使,希伯来语中名叫阿巴顿,希腊语名叫阿波伦。 (Abyssos )
12 Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.
第一场灾祸过去了。但还有两场灾祸即将到来!
13 Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah.
第六位天使吹响号角,我听到上帝面前金坛的四角发出一个声音,
14 Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.”
对拿着号角的第六位天使说:“把捆绑在幼发拉底大河的那四位天使放了!”
15 Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na’yan Adam.
那四位天使于是被释放,他们已经做好准备,要在具体的某年某月某日某时,消灭三分之一的人类。
16 Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu.
我听到马兵的数目是 2 亿人。
17 Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa.
在幻象中,我看到那些马和骑士是这样的:骑士身穿火红、深蓝和黄色的胸甲;马头好像狮子,马口喷出火、烟和硫磺。
18 Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu.
马口喷出的火、烟和硫磺引发了三次瘟疫,杀死三分之一人类。
19 Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.
这些马的力量存在于它们的口中和尾巴上。他们的尾巴像蛇头,用来伤害人。
20 Sauran’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba.
那些未被瘟疫杀死的人类,仍然不为自己的所作所为而悔改,不肯停止崇拜魔鬼以及用金、银、铜、石头、木头做成的,不能看、不能听、也不能走路的神像。
21 Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
他们也不会为自己的谋杀、邪术、淫乱和偷盗而悔改。