< Ru’uya ta Yohanna 8 >

1 Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin sa’a.
As soon as the Lamb had broken the seventh seal, there was silence in Heaven for, it might be, half-an-hour.
2 Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai.
Then I saw the seven angels who stand before God, and seven trumpets were given to them.
3 Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin.
Next, another angel came and stood at the altar with a golden censer in his hand; and a great quantity of incense was given to him, to mingle with the prayers of all Christ’s People upon the golden altar before the throne.
4 Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan.
The smoke of the incense ascended, with the prayers of Christ’s People, from the hand of the angel before God.
5 Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa.
Then the angel took the censer, and filled it with fire from the altar, and threw it down upon the earth; and there followed ‘peals of thunder, cries, flashes of lightning,’ and an earthquake.
6 Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su.
Then the seven angels holding the seven trumpets prepared to blow their blasts.
7 Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
The first blew; and there came hail and fire mixed with blood, and it fell upon the earth. A third part of the earth was burnt up, and a third of the trees, and every blade of grass.
8 Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini,
Then the second angel blew; and what appeared to be a great mountain, burning, was hurled into the sea. A third of the sea became blood,
9 kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka.
and a third part of all created things that are in the sea — that is, of all living things — died, and a third of the ships was destroyed.
10 Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa
Then the third angel blew; and there fell from the heavens a great star, burning like a torch. It fell upon a third of the rivers and upon the springs.
11 sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
(The star is called ‘Wormwood.’) A third of the water became bitter as wormwood, and so bitter was the water that many died from drinking it.
12 Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare.
Then the fourth angel blew; and a third of the sun and a third of the moon and a third of the stars were blasted, so that a third of them was eclipsed, and for a third part of the day there was no light, and at night it was the same.
13 Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!”
And, in my vision, I heard an eagle flying in mid-heaven and crying in a loud voice — ‘Woe, woe, woe for all who live on the earth, at the other trumpet-blasts of the three angels who have yet to blow.’

< Ru’uya ta Yohanna 8 >