< Ru’uya ta Yohanna 6 >

1 Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!”
And I saw when the Lamb opened one of the seals, and I heard one of the four animate beings saying, as with a voice of thunder, Come and see.
2 Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara.
And I saw, and behold a white horse; and He that sat upon it had a bow, and a crown was given Him, and He went forth conquering and to conquer.
3 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!”
And when He opened the second seal, I heard the second animal saying, Come and see.
4 Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.
And there came out another horse, which was red: and it was given to him, that sat upon it, to take peace from the earth, that they should kill one another: and there was given him a great sword.
5 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa.
And when He opened the third seal, I heard the third animal say, Come and see. And I beheld, and lo, a black horse, and he that sat upon it had a balance in his hand.
6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”
And I heard a voice in the midst of the four animals saying, One measure of wheat for a denary, and but three measures of barley for a denary: but see that thou hurt not the oil and the wine.
7 Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!”
And when He opened the fourth seal, I heard the voice of the fourth animal saying, Come and see.
8 Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya. (Hadēs g86)
And I saw, and behold a pale horse, and the name of him that sat upon it was Death, and Hades followed him: and power was given them to slay a fourth part of the earth, by sword, and by famine, and by pestilence, and by wild beasts. (Hadēs g86)
9 Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi.
And when He opened the fifth seal, I saw under the altar the souls of those that had been slain for the word of God, and for the testimony which they maintained.
10 Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?”
And they cried with a loud voice, saying, How long, O Lord, holy and true, dost thou not judge and avenge our blood on those that dwell upon the earth?
11 Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.
And white robes were given to each of them, and it was told them to rest a little while longer, till the number of their fellow-servants, and their brethren that should be killed as they were, should be complete.
12 Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini,
And I saw when He opened the sixth seal, and behold there was a great earthquake, and the sun became black as sack-cloth of hair, and the moon was red as blood;
13 taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi.
and the stars of heaven fell to the earth, as a fig-tree droppeth it's unripe figs, when shaken by a strong wind;
14 Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.
and the heaven passed away as a book rolled up, and every mountain and island were moved out of their places:
15 Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka.
and the kings of the earth, and the grandees, and the rich men, and the chief captains, and the mighty men, and every slave, and every free man, hid themselves in the caverns and in the rocks of the mountains;
16 Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan!
and said to the mountains and to the rocks, "Fall upon us, and hide us from the face of Him that sitteth on the throne, and from the wrath of the Lamb:
17 Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”
for the great day of his wrath is come, and who can stand before Him?"

< Ru’uya ta Yohanna 6 >