< Ru’uya ta Yohanna 4 >

1 Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”
Derefter saa jeg, og se, der var en Dør aabnet i Himmelen, og den første Røst, hvilken jeg havde hørt som af en Basun, der talte med mig, sagde: Stig herop, og jeg vil vise dig, hvad der skal ske herefter.
2 Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa.
Straks henryktes jeg i Aanden; og se, en Trone stod i Himmelen, og en sad paa Tronen,
3 Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin.
og den siddende var at se til ligesom Jaspissten og Sarder, og der var en Regnbue omkring Tronen, at se til ligesom Smaragd.
4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu.
Og omkring Tronen var der fire og tyve Troner, og paa Tronerne sad der fire og tyve Ældste, iførte hvide Klæder og med Guldkranse paa deres Hoveder.
5 Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.
Og fra Tronen udgaar der Lyn og Røster pg Tordener, og syv Ildfakler brænde foran Tronen, hvilke ere de syv Guds Aander.
6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.
Og foran Tronen er der som et Glarhav, ligesom Krystal, og midt for Tronen og rundt om Tronen fire levende Væsener, fulde af Øjne fortil og bagtil.
7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama.
Og det første Væsen ligner en Løve; og det andet Væsen ligner en Okse; og det tredje Væsen har Ansigt som et Menneske; og det fjerde Væsen ligner en flyvende Ørn.
8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
Og de fire Væsener have hvert især seks Vinger, rundt om og indadtil ere de fulde af Øjne; og uden Ophør sige de Dag og Nat: Hellig, hellig, hellig er Herren, Gud, den almægtige, han, som var, og som er, og som kommer!
9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, (aiōn g165)
Og naar Væsenerne give Ære og Pris og Tak til ham, som sidder paa Tronen, ham, som lever i Evighedernes Evigheder, (aiōn g165)
10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, (aiōn g165)
da falde de fire og tyve Ældste ned for ham, som sidder paa Tronen, og tilbede ham, som lever i Evighedernes Evigheder, og lægge deres Kranse ned for Tronen og sige: (aiōn g165)
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”
Værdig er du, vor Herre og Gud, til at faa Prisen og Æren og Magten; thi du har skabt alle Ting, og paa Grund af din Villie vare de, og bleve de skabte.

< Ru’uya ta Yohanna 4 >