< Ru’uya ta Yohanna 4 >
1 Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”
Potom jsem viděl, a aj, dveře otevříny byly v nebi, a hlas první, kterýž jsem byl slyšel jako trouby, an mluví se mnou, řkoucí: Vstup sem, a ukážiť, co se má díti potom.
2 Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa.
A hned byl jsem u vytržení ducha, a aj, trůn postaven byl na nebi, a na trůnu jeden seděl.
3 Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin.
A ten, jenž seděl, podoben byl obličejem kameni jaspidu a sardiovi; a vůkol toho trůnu byla duha, na pohledění podobná smaragdu.
4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu.
A okolo toho trůnu bylo stolic čtyřmecítma, a na těch stolicích viděl jsem čtyřmecítma starců sedících, oblečených v roucha bílá. A měli na hlavách svých koruny zlaté.
5 Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.
A z toho trůnu pocházelo blýskání, a hromobití, a hlasové. A sedm lamp ohnivých hořících před trůnem, jenž jsou sedm Duchů Božích.
6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.
A před trůnem bylo moře sklené, podobné křišťálu, a uprostřed trůnu a vůkol trůnu čtvero zvířat, plných očí zpředu i zzadu.
7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama.
A zvíře první podobné bylo lvu, a druhé zvíře podobné teleti, a třetí zvíře mající tvárnost jako člověk, a čtvrté zvíře podobné orlu letícímu.
8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
A jedno každé z těch čtyř zvířat mělo šest křídel okolo, a vnitř plná byla očí, a neměla odpočinutí dnem i nocí, říkajíce: Svatý, svatý, svatý Pán Bůh všemohoucí, kterýž byl, a jest, i přijíti má.
9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, (aiōn )
A když ta zvířata vzdávala slávu a čest i díků činění sedícímu na trůnu, živému na věky věků, (aiōn )
10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, (aiōn )
Padlo těch čtyřmecítma starců před obličejem sedícího na trůnu, a klanělo se živému na věky věků, a metali koruny své před trůnem, řkouce: (aiōn )
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”
Hoden jsi, Pane, přijíti slávu, a čest, i moc; nebo ty jsi stvořil všecky věci, a pro vůli tvou trvají, i stvořeny jsou.