< Ru’uya ta Yohanna 22 +
1 Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon,
And he showed me the river of the Water of Life, clear as crystal, Flowing out from the throne of God, and of the Lamb,
2 yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da’ya’ya goma sha biyu, yana ba da’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne.
In the middle of the broad street of the City. On each side of the river was a Tree of Life, Bearing twelve kinds of fruit, Each month yielding its own fruit. And the leaves of the tree Were for the healing of the nations.
3 Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima.
And there will be no more curse But in it will be the throne of God and of the Lamb. And his slaves will serve and worship him.
4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu.
They will see his face.
5 Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin. (aiōn )
His name will need no lamplight nor sunlight, Because the Lord God will give them light; And they will reign forever and ever. (aiōn )
6 Mala’ikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki mala’ikansa, don yă nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.”
Then he said to me. "These words may be trusted, and are true. the Lord, the God of the spirits of the prophets, has sent his angel to show his slaves what must soon take place.
7 “Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.”
"And behold, I am coming quickly. Blessed is he who keeps the words of the prophecy of this book."
8 Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada.
And I, John, am he who heard and saw these things. And after I heard and saw them, I fell down to worship at the feet of the angel who showed them to me.
9 Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”
But he said to me. "See thou do it not. I am only a fellow slave with you and your brothers, the prophets, and with those who keep the words of this Book. "WORSHIP GOD!"
10 Sa’an nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa.
And he said to me, "Do not seal up the words of the prophecy of this book; for the crisis is near.
11 Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”
He who is wicked, let him be wicked still; He who is filthy, let him be filthy still; He who is righteous, lit him practise righteousness still; And he who is holy, let him be made holy still.
12 “Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.
Behold, I come quickly; and my reward is with me, To give to each man what his actions merit.
13 Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.
I am the Alpha and the Omega, The First and the Last, The Beginning and the End.
14 “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi.
"Blessed are they who wash their robes, so that they may have right to the Tree of Life, and may enter in by the gates into the City.
15 Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.
Without are the dogs, the sorcerers, the immoral, the murderers, the idolaters, and all who live and make a lie.
16 “Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.”
"I, Jesus, have sent my angel to give you this testimony for the churches. I am the root and offspring of David, the bright and morning Star.
17 Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta.
"And the Spirit and the Bride say ‘Come!’ And let him who hears, say’Come!’ And let him who thirsts, come; And whoever wills, let him take the Water of Life freely."
18 Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan.
I testify to every man who hears the words of the prophecy of this book. If any man shall add to them, God will add to him the plagues which are written in this book;
19 Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.
and if any man shall take away from the words of the book of this prophecy, God will take away his share in the Tree of Life, and in the Holy City, about which this book is written.
20 Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu!
He who testifies this says, "Yea, I am coming quickly." Amen! Come, Lord Jesus!
21 Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.
The grace of the Lord Jesus Christ be with the saints!