< Ru’uya ta Yohanna 21 >
1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku.
And I saw a new Heaven and a new earth; for the first Heaven and the first earth were gone, and the sea no longer exists.
2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta.
And I saw the holy city, the new Jerusalem, coming down out of Heaven from God and made ready like a bride attired to meet her husband.
3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu.
And I heard a loud voice, which came from the throne, say, "God's dwelling place is among men and He will dwell among them and they shall be His peoples. Yes, God Himself will be among them.
4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
He will wipe every tear from their eyes. Death shall be no more; nor sorrow, nor wail of woe, nor pain; for the first things have passed away."
5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”
Then He who was seated on the throne said, "I am re-creating all things." And He added, "Write down these words, for they are trustworthy and true."
6 Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai.
He also said, "They have now been fulfilled. I am the Alpha and the Omega, the Beginning and the End. To those who are thirsty I will give the privilege of drinking from the well of the Water of Life without payment.
7 Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana.
All this shall be the heritage of him who overcomes, and I will be his God and he shall be one of My sons.
8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” (Limnē Pyr )
But as for cowards and the unfaithful, and the polluted, and murderers, fornicators, and those who practise magic or worship idols, and all liars--the portion allotted to them shall be in the Lake which burns with fire and sulphur. This is the Second Death." (Limnē Pyr )
9 Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.”
Then there came one of the seven angels who were carrying the seven bowls full of the seven last plagues. "Come with me," he said, "and I will show you the Bride, the Lamb's wife."
10 Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah.
So in the Spirit he carried me to the top of a vast, lofty mountain, and showed me the holy city, Jerusalem, coming down out of Heaven from God,
11 Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi.
and bringing with it the glory of God. It shone with a radiance like that of a very precious stone--such as a jasper, bright and transparent.
12 Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila.
It has a wall, massive and high, with twelve large gates, and in charge of the gates were twelve angels. And overhead, above the gates, names were inscribed which are those of the twelve tribes of the descendants of Israel.
13 Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma.
There were three gates on the east, three on the north, three on the south, and three on the west.
14 An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.
The wall of the city had twelve foundation stones, and engraved upon them were twelve names--the names of the twelve Apostles of the Lamb.
15 Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa.
Now he who was speaking to me had a measuring-rod of gold, with which to measure the city and its gates and its wall.
16 Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke.
The plan of the city is a square, the length being the same as the breadth; and he measured the city furlong by furlong, with his measuring rod--it is twelve hundred miles long, and the length and the breadth and the height of it are equal.
17 Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi.
And he measured the wall of it--a wall of a hundred and forty-four cubits, according to human measure, which was also that of the angel.
18 An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.
The solid fabric of the wall was jasper; and the city itself was made of gold, resembling transparent glass.
19 Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu,
As for the foundation-stones of the city wall, which were beautified with various kinds of precious stones, the first was jasper, the second sapphire, the third chalcedony, the fourth emerald, the fifth sardonyx, the sixth sardius,
20 na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis.
the seventh chrysolite, the eighth beryl, the ninth topaz, the tenth chrysoprase, the eleventh jacinth, the twelfth amethyst.
21 Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.
And the twelve gates were twelve pearls; each of them consisting of a single pearl. And the main street of the city was made of pure gold, resembling transparent glass.
22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin.
I saw no sanctuary in the city, for the Lord God, the Ruler of all, is its Sanctuary, and so is the Lamb.
23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin.
Nor has the city any need of the sun or of the moon, to give it light; for the glory of God has shone upon it and its lamp is the Lamb.
24 Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin.
The nations will live their lives by its light; and the kings of the earth are to bring their glory into it.
25 Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba.
And in the daytime (for there will be no night there) the gates will never be closed;
26 Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin.
and the glory and honor of the nations shall be brought into it.
27 Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.
And no unclean thing shall ever enter it, nor any one who is guilty of base conduct or tells lies, but only they whose names stand recorded in the Lamb's Book of Life.