< Ru’uya ta Yohanna 20 >
1 Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. (Abyssos )
И видех Ангела сходяща с небесе, имеюща ключь бездны и уже велико в руце своей: (Abyssos )
2 Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.
и ят змия, змия древняго, иже есть диавол и сатана, и связа и на тысящу лет,
3 Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. (Abyssos )
и в бездну затвори его, и заключи его, и запечатле над ним, да не прельстит ктому языки, дондеже скончается тысяща лет: и по сих подобает ему отрешену быти на мало время. (Abyssos )
4 Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.
И видех престолы и седящыя на них, и суд дан бысть им: и душы растесаных за свидетелство Иисусово и за слово Божие, иже не поклонишася зверю, ни иконе его, и не прияша начертания на челех своих и на руце своей. И ожиша и воцаришася со Христом тысящу лет:
5 (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
прочии же мертвецы не ожиша, дондеже скончается тысяща лет. Се воскресение первое.
6 Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
Блажен и свят, иже имать часть в воскресении первем: на нихже смерть вторая не имать области, но будут иерее Богу и Христу и воцарятся с Ним тысящу лет.
7 Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake,
И егда скончается тысяща лет, разрешен будет сатана от темницы своея и изыдет прельстити языки сущыя на четырех углех земли, Гога и Магога, собрати их на брань, ихже число яко песок морский.
8 zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.
И взыдоша на широту земли и обыдоша святых стан и град возлюбленный.
9 Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.
И сниде огнь от Бога с небесе и пояде я:
10 Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn , Limnē Pyr )
и диавол льстяй их ввержен будет в езеро огненно и жупелно, идеже зверь и лживый пророк: и мучени будут день и нощь во веки веков. (aiōn , Limnē Pyr )
11 Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.
И видех престол велик бел и Седящаго на нем, Егоже от лица бежа небо и земля, и место не обретеся им.
12 Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.
И видех мертвецы малыя и великия стоящя пред Богом, и книги разгнушася: и ина книга отверзеся, яже есть животная: и суд прияша мертвецы от написаных в книгах, по делом их.
13 Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. (Hadēs )
И даде море мертвецы своя, и смерть и ад даста своя мертвецы: и суд прияша по делом своим, (Hadēs )
14 Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. (Hadēs , Limnē Pyr )
и смерть и ад ввержена быста в езеро огненное. И се есть вторая смерть. (Hadēs , Limnē Pyr )
15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. (Limnē Pyr )
И иже не обретеся в книзе животней написан, ввержен будет в езеро огненное. (Limnē Pyr )