< Ru’uya ta Yohanna 20 >

1 Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. (Abyssos g12)
後,我看見一位天使從天降下,手持深淵的鑰匙和一條大鎖鏈。 (Abyssos g12)
2 Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu.
他捉住了那龍,那古蛇,就是魔鬼--撒殫,把牠綑起來,共一千年之久;
3 Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci. (Abyssos g12)
將牠拋到深淵裏,關起來,加上封條,免得牠再迷惑萬民,直到滿了一千年,此後應該釋放牠一個短時辰。 (Abyssos g12)
4 Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.
我又看見一些寶座,有些人在上面坐著,賜給了他們審判的權柄,他們就是那些為給耶穌作證,並為了天主的話被斬首之人的靈魂;還有那些沒有朝拜那獸,也沒有朝拜獸像,並在自己的額上或手上也沒有接受牠印號的人,都活了過來,同基督一起為王一千年。
5 (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.
這是第一次復活。其餘的死者沒有活過來,直到那一千年滿了。
6 Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
於第一次復活有分的人是有福的,是聖潔的。第二次的死亡對這些人無能為力;他們將作天主和基督的司祭,並同他一起為王一千年。
7 Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake,
及至一千年滿了,撒殫就要從監牢裏被釋放出來。
8 zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.
他一出來便去迷惑地上四極的萬民,就是哥格和瑪哥格;他聚集他們準備作戰,他們的數目有如海濱的沙粒。
9 Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.
於是他們上到那廣大的地區,圍困了眾聖徒的營幕和蒙愛的城邑;但是有火自天上,從天主那裏降下,吞滅了他們。
10 Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin. (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
迷惑他們的魔鬼,也被投入那烈火與硫磺的坑中,就是那獸和那位假先知所在的地方,他們必要日夜受苦,至於無窮之世。 (aiōn g165, Limnē Pyr g3041 g4442)
11 Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.
以後,我看見了一個潔白的大寶座,和坐於其上的那位;地和天都從他面前消失不見了,再也找不到它們的地方了。
12 Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.
我又看見死過的人,無論大小,都站在寶座前,案卷就展開了;還有另一本書,即生命冊也展開了,死過的人都按那案卷上所記錄的,照他們的行為受了審判。
13 Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. (Hadēs g86)
海洋把其中的死者交出,死亡和陰府都把其中的死者交出,人人都按照自己的行為受了審判。 (Hadēs g86)
14 Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
然後死亡和陰府也被投入火坑,這火坑就是第二次死亡。 (Hadēs g86, Limnē Pyr g3041 g4442)
15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan. (Limnē Pyr g3041 g4442)
凡是沒有記載在生命冊上的人,就被投入火坑中。 (Limnē Pyr g3041 g4442)

< Ru’uya ta Yohanna 20 >