< Ru’uya ta Yohanna 2 >

1 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.
''Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Afisus, ka rubuta: 'Wadannan sune kalmomin wanda ke rike da taurari bakwai a cikin hannun damarsa. wanda yake tafiya a tsakanin zankayen fitilun zinari bakwai,
2 Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne.
''Na san abubuwan da ka yi, da famar ka, da hakurinka da jimirinka. Na sani ba ka jimrewa miyagun mutane, na sani ka gwada wadanda suka ce da kansu, su manzanni ne, amma ba haka ba, ka tarar da su makaryata.
3 Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
Na san kana da tsawon jimrewa, kuma ka sha wahala sosai sabili da sunana, kuma baka gaji ba.
4 Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko.
Amma ga rashin jin dadi na da kai, ka bar kaunar ka ta fari.
5 Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake.
Domin haka ka tuna daga inda ka fadi. Ka tuba ka yi abubuwan da ka yi da fari. Sai fa ka tuba, zan zo maka in kuma cire fitilar ka daga mazauninta.
6 Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.
Amma kana da wannan: Ka tsani abubuwan da Nikolatawa suka yi, wanda nima na tsana.
7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.
wanda yake da kunnen ji ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bashi dama ya ci daga itacen rai, wanda ke cikin firdausin Allah.””
8 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.
Zuwa ga mala'ikan da ke Ikilisiliyar Samirna rubuta: 'Wadannan su ne kalmomin wanda yake shine farko shine karshe, wanda ya mutu ya sake rayuwa kuma.
9 Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.
''Na san wahalun ka da talaucin ka amma kana da arziki. Nasan masu bata suna wadanda suke cewa su Yahudawa ne, amma ba haka suke ba. Su majami'ar Shaidan ne.
10 Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
Kada ka ji tsoron wahalar da zaka fuskanta nan gaba. Duba! Shaidan yana gab da jefa wadansun ku cikin kurkuku, domin a gwada ku, kuma zaku sha wahala ta kwana goma. Kuyi aminci har ga mutuwa zan baku rawanin rai.
11 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.
wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Shi wanda yayi nasara ba zai cutu a mutuwa ta biyu ba.””
12 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Fergamum, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin wannan wanda yake da takobi mai kaifi biyu.
''Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Burgamas rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda ya ke da takobi mai kaifi biyu;
13 Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama.
''Na san inda kake zama can inda kursiyin shaidan yake. Duk da haka ka rike sunana da karfi, na sani baka yi musun bangaskiyar ka da ni ba, ko a lokacin Antifas mashaidina, amintaccena, wanda aka kashe a tsakaninku, can inda shaidan yake zama.
14 Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci.
Amma ga rashin jin dadi na kadan da kai: Kana da wadansu da suke rike da koyarwar Bil'amu kamkam, wanda ya koya wa Balak ya sa abin tuntubi gaban 'ya'yan Isra'ila, domin su ci abincin da aka mika wa gumaka kuma suyi fasikanci.
15 Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa.
Hakannan kuma wasunku sun rike koyarwar Nikolatawa kamkam.
16 Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina.
Sabili da haka ka tuba! Idan ka ki zan zo gare ka da sauri, kuma in yi yaki gaba da su da takobi dake cikin bakina.
17 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.
Bari wanda yake da kunne ya sauriri abin da Ruhu yake fadawa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bada wata boyayyar manna, kuma zan bashi farin dutse da sabon suna a rubuce a kan dutsen, suna wanda ba wanda ya sani, sai shi wanda ya karbe shi.””
18 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Tiyatira, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomin Ɗan Allah, wanda idanunsa suna kama da harshen wuta wanda kuma ƙafafunsa suna kama da tagullar da aka goge.
Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Tiyatira rubuta: 'Wadannan sune kalamomin Dan Allah, wanda yake da idanu kamar harshen wuta; sawayen kamar gogaggiyar tagulla:
19 Na san ayyukanka, ƙaunarka da bangaskiyarka, hidimarka da daurewarka, kuma cewa kana yin abubuwa a yanzu fiye da abin da ka yi da farko.
''Na san abin da ka yi, kaunar ka, da bangaskiya da hidima da tsawon jimrewar ka. Na san abinda ka yi bada dadewa ba ya fi abinda ka yi da fari.
20 Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka.
Amma ga rashin jin dadi na da kai: Kana hakurce wa matar nan Yezebel, wadda take kiran kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta, ta rudi bayina suyi fasikanci kuma su ci abincin da aka mika wa gumaka sadaka.
21 Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya.
Na bata lokaci domin ta tuba amma bata so ta tuba da fasikancin ta.
22 Don haka zan jefa ta a kan gadon wahala, zan kuma sa waɗanda suke zina da ita, su sha azaba ƙwarai, sai dai in sun tuba daga hanyoyinta.
Duba! zan jefa ta a kan gadon jinya, wadanda kuma suka yi zina da ita za su shiga babbar wahala, sai dai in sun tuba daga ayukan ta.
23 Zan kashe’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa.
Zan buga 'ya'yanta da mutuwa, kuma dukan ikilisiyoyi zasu san cewa nine wanda nake bincike tunani da zukata. Zan ba kowanen ku bisa ga ayyukansa.
24 Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba.
Amma ga sauran ku dake cikin Tayatira, ga kowanen ku wanda bai rike wannan koyarwar ba, kuma bai san abinda wadansu suke kira zurfafan abubuwan Shaidan ba—ga ku na ce ban sa muku wata nawaya ba.'
25 Sai dai ku riƙe abin da kuke da shi har sai na zo.’
Duk da haka dole ku tsaya da karfi har in zo.
26 Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai.
Wanda yayi nasara da wanda ya yi abin da na yi har karshe, a gareshi zan bada iko akan al'ummai
27 ‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’kamar yadda na karɓi iko daga Ubana.
Zai yi mulkin su da sandar karfe, zai farfasa su kamar randunan yumbu.”
28 Zan kuma ba shi tauraron asubahi.
Kamar yadda na karba daga wurin Ubana, ni kuma zan bashi tauraron asubahi.
29 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.
Bari wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fadawa ikilisiyioyi.””

< Ru’uya ta Yohanna 2 >