< Ru’uya ta Yohanna 16 >
1 Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”
2 Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.
3 Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.
4 Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini.
5 Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;
6 gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”
7 Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”
8 Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta.
9 Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.
10 Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba
11 suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.
12 Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas.
13 Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan.
14 Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.
15 “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”
16 Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.
17 Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!”
18 Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce.
19 Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa.
20 Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba.
21 Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.