< Ru’uya ta Yohanna 14 >

1 Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu.
Et je vis: et voici l’Agneau se tenant sur la montagne de Sion, et avec lui 144 milliers, ayant son nom et le nom de son Père écrits sur leurs fronts.
2 Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu.
Et j’entendis une voix venant du ciel, comme une voix de grandes eaux et comme une voix d’un grand tonnerre; et la voix que j’entendis était comme de joueurs de harpe, jouant de leurs harpes;
3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.
et ils chantent un cantique nouveau devant le trône, et devant les quatre animaux et les anciens. Et personne ne pouvait apprendre le cantique, sinon les 144 milliers qui ont été achetés de la terre.
4 Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.
Ce sont ceux qui ne se sont point souillés avec les femmes, car ils sont vierges; ce sont ceux qui suivent l’Agneau où qu’il aille; ceux-ci ont été achetés d’entre les hommes, des prémices à Dieu et à l’Agneau;
5 Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.
et il n’a pas été trouvé de mensonge dans leur bouche; ils sont irréprochables.
6 Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. (aiōnios g166)
Et je vis un [autre] ange volant par le milieu du ciel, ayant l’évangile éternel pour l’annoncer à ceux qui sont établis sur la terre, et à toute nation et tribu et langue et peuple, (aiōnios g166)
7 Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
disant à haute voix: Craignez Dieu et donnez-lui gloire, car l’heure de son jugement est venue; et rendez hommage à celui qui a fait le ciel et la terre et la mer et les fontaines d’eaux.
8 Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”
Et un autre, un second ange, suivit, disant: Elle est tombée, elle est tombée, Babylone la grande, qui, du vin de la fureur de sa fornication, a fait boire à toutes les nations.
9 Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu,
Et un autre, un troisième ange, suivit ceux-là, disant à haute voix: Si quelqu’un rend hommage à la bête et à son image, et qu’il reçoive une marque sur son front ou sur sa main,
10 shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon.
lui aussi boira du vin de la fureur de Dieu, versé sans mélange dans la coupe de sa colère; et il sera tourmenté dans le feu et le soufre devant les saints anges et devant l’Agneau.
11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” (aiōn g165)
Et la fumée de leur tourment monte aux siècles des siècles; et ils n’ont aucun repos, ni jour, ni nuit, ceux qui rendent hommage à la bête et à son image, et si quelqu’un prend la marque de son nom. (aiōn g165)
12 Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.
Ici est la patience des saints; [ici], ceux qui gardent les commandements de Dieu et la foi de Jésus.
13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
Et j’entendis une voix venant du ciel, disant: Écris: Bienheureux les morts qui meurent dans le Seigneur, dorénavant. Oui, dit l’Esprit, afin qu’ils se reposent de leurs travaux, car leurs œuvres les suivent.
14 Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.
Et je vis: et voici une nuée blanche, et sur la nuée [quelqu’un] assis, semblable au Fils de l’homme, ayant sur sa tête une couronne d’or et dans sa main une faucille tranchante.
15 Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.”
Et un autre ange sortit du temple, criant à haute voix à celui qui était assis sur la nuée: Lance ta faucille et moissonne; car l’heure de moissonner est venue, parce que la moisson de la terre est desséchée.
16 Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.
Et celui qui était assis sur la nuée mit sa faucille sur la terre, et la terre fut moissonnée.
17 Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi.
Et un autre ange sortit du temple qui est dans le ciel, ayant lui aussi une faucille tranchante.
18 Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin’ya’yan inabin sun nuna.”
Et un autre ange, ayant pouvoir sur le feu, sortit de l’autel et, en jetant un grand cri, il cria à celui qui avait la faucille tranchante, disant: Lance ta faucille tranchante et vendange les grappes de la vigne de la terre, car ses raisins ont mûri.
19 Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah.
Et l’ange mit sa faucille sur la terre, et vendangea la vigne de la terre, et jeta [les grappes] dans la grande cuve du courroux de Dieu.
20 Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.
Et la cuve fut foulée hors de la ville; et de la cuve il sortit du sang jusqu’aux mors des chevaux, sur un espace de 1 600 stades.

< Ru’uya ta Yohanna 14 >