< Ru’uya ta Yohanna 13 >
1 Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo.
2 Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma.
3 Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar.
4 Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?”
5 Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu.
6 Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama.
7 Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma.
8 Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.
9 Duk mai kunne ji, bari yă ji.
10 Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka.
11 Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji.
12 Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta.
13 Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane.
14 Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu.
15 Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada.
16 Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta,’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi,
17 don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta.
18 Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.