< Ru’uya ta Yohanna 12 >

1 Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta.
And a great sign appeared in heaven: a woman clothed in the sun, with the moon under her feet and a crown of twelve stars on her head.
2 Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa.
She was pregnant and crying out in the pain and agony of giving birth.
3 Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa.
Then another sign appeared in heaven: a huge red dragon with seven heads, ten horns, and seven royal crowns on his heads.
4 Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.
His tail swept a third of the stars from the sky, tossing them to the earth. And the dragon stood before the woman who was about to give birth, ready to devour her child as soon as she gave birth.
5 Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa.
And she gave birth to a son, a male child, who will rule all the nations with an iron scepter. And her child was caught up to God and to His throne.
6 Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.
And the woman fled into the wilderness, where God had prepared a place for her to be nourished for 1,260 days.
7 Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani.
Then a war broke out in heaven: Michael and his angels fought against the dragon, and the dragon and his angels fought back.
8 Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama.
But the dragon was not strong enough, and no longer was any place found in heaven for him and his angels.
9 Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya.
And the great dragon was hurled down—that ancient serpent called the devil and Satan, the deceiver of the whole world. He was hurled to the earth, and his angels with him.
10 Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa.
And I heard a loud voice in heaven saying: “Now have come the salvation and the power and the kingdom of our God, and the authority of His Christ. For the accuser of our brothers has been thrown down— he who accuses them day and night before our God.
11 Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.
They have conquered him by the blood of the Lamb and by the word of their testimony. And they did not love their lives so as to shy away from death.
12 Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”
Therefore rejoice, O heavens, and you who dwell in them! But woe to the earth and the sea; with great fury the devil has come down to you, knowing he has only a short time.”
13 Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji.
And when the dragon saw that he had been thrown to the earth, he pursued the woman who had given birth to the male child.
14 Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba.
But the woman was given two wings of a great eagle to fly from the presence of the serpent to her place in the wilderness, where she was nourished for a time, and times, and half a time.
15 Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya.
Then from the mouth of the serpent spewed water like a river to overtake the woman and sweep her away in the torrent.
16 Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa.
But the earth helped the woman and opened its mouth to swallow up the river that had poured from the dragon’s mouth.
17 Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
And the dragon was enraged at the woman, and went to make war with the rest of her children, who keep the commandments of God and hold to the testimony of Jesus. And the dragon stood on the shore of the sea.

< Ru’uya ta Yohanna 12 >