< Ru’uya ta Yohanna 11 >

1 Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can.
And there was given me a reed like to a staff, a voice saying: Rise, and measure the temple of God, and the altar, and them that worship therein;
2 Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42.
but the court which is outside the temple, leave out, and measure it not, for it hath been given to the gentiles; and the holy city will they tread under foot forty-two months.
3 Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.”
And I will give power to my two witnesses, and they shall prophesy a thousand two hundred and sixty days, clothed in sackcloth.
4 Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya.
These are the two olive-trees, and the two candlesticks, which stand before the Lord of the earth.
5 Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu.
And if any one designs to hurt them, fire goeth out of their mouth, and devoureth their enemies; and if any one designs to hurt them, he must in this manner be killed.
6 Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.
These have power to shut heaven, that it rain not in the days of their prophecy; and have power over the waters, to turn them to blood, and to smite the earth with every plague, as often as they will.
7 To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. (Abyssos g12)
And when they shall have finished their testimony, the beast that cometh up out of the abyss will make war against them, and will overcome them, and kill them. (Abyssos g12)
8 Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu.
And their dead bodies shall lie in the street of the great city, which spiritually is called Sodom and Egypt, where their Lord also was crucified.
9 Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su.
And some from among the peoples, and tribes, and tongues, and nations, will look upon their dead bodies three days and a half, and will not suffer their dead bodies to be put into a tomb.
10 Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya.
And they that dwell upon the earth will rejoice over them, and make merry, and will send gifts to one another, because these two prophets tormented those who dwelt on the earth.
11 Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su.
And after three days and a half the spirit of life from God entered into them, and they stood upon their feet; and great fear fell upon those who saw them.
12 Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo.
And they heard a loud voice from heaven, saying to them, Come up hither; and they went up into heaven in a cloud; and their enemies beheld them.
13 A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama.
And in that hour there was a great earthquake, and the tenth part of the city fell, and in the earthquake were slain seven thousand men; and the rest became afraid, and gave glory to the God of heaven.
14 Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba.
The second woe is past; behold, the third woe cometh quickly.
15 Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” (aiōn g165)
And the seventh angel sounded, and there followed loud voices in heaven, saying, The kingdom of the world is become the kingdom of our Lord and of his Christ, and he will reign for ever and ever. (aiōn g165)
16 Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada,
And the twenty-four elders, who sat before God on their thrones, fell upon their faces, and worshipped God,
17 suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki.
saying, We give thanks to thee, O Lord God Almighty, who art and who wast, because thou hast taken thy great power, and hast reigned.
18 Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”
And the nations were enraged, and thy wrath is come, and the time of the dead to be judged, and to give the reward to thy servants the prophets, and to the saints, and to them that fear thy name, the small and the great; and to destroy the destroyers of the earth.
19 Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.
And the temple of God was opened in heaven, and the ark of his covenant was seen in his temple; and there were lightnings, and voices, and thunders, and an earthquake, and a great hailstorm.

< Ru’uya ta Yohanna 11 >