< Ru’uya ta Yohanna 1 >
1 Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,
Wannan shine wahayin Yesu Almasihu da Allah ya bashi ya nuna wa bayinsa abinda zai faru ba da dadewa ba. Ya bayyana wannan ta wurin aiko da mala'ikansa ga bawansa Yahaya.
2 wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi.
Yahaya yayi shaida akan abinda ya gani game da maganar Allah da kuma shaidar da aka bayar game da Yesu Almasihu.
3 Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa.
Mai albarka ne wanda ke karanta littafin nan da murya mai karfi, da kuma wadanda ke sauraron kalmomin wannan annabci kuma suke biyayya da abinda aka rubuta a ciki, domin kuwa lokaci ya kusato.
4 Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa,
Ni Yahaya, zuwa ga ikilisiyoyi bakwai na kasar Asiya: alheri zuwa gare ku da salama daga wanda ke yanzu, wanda ya kuma kasance a da, shi ne kuma mai zuwa nan gaba, kuma daga ruhohin nan bakwai da ke gaban kursiyinsa,
5 da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa,
kuma daga Yesu Almasihu, wanda ke amintaccen mashaidi, dan fari na tashi daga cikin matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya. Ga wanda ya ke kaunar mu ya kuma kwance mu daga daurin zunubanmu ta wurin jininsa,
6 ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin. (aiōn )
ya maishe mu masu mulki, firistoci na Allahnsa da Ubansa - daukaka da iko su tabbata gare shi har abada abadin, Amin. (aiōn )
7 “Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.”
Duba yana zuwa tare da gizagizai, kowane ido zai gan shi, har ma da wadanda suka soke shi. Haka kuma dukkan kabilun duniya za su yi makoki saboda da shi. I, Amin.
8 “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”
“Nine na farko da na karshe”, in ji Ubangiji Allah, “Wanda yake shine a yanzu, shine wanda ya kasance a da, kuma shi ne mai zuwa nan gaba, Mai iko duka.”
9 Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu.
Ni, Yahaya- dan'uwan ku da wanda ke tarayya daku cikin shan wahala, da mulki da tsawon jimrewa wadanda ke cikin Yesu - ina tsibirin da ake kira Batmusa saboda maganar Allah da kuma shaida game da Yesu.
10 A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho,
Ina cikin Ruhu a ranar Ubangiji. Sai naji wata murya mai karfi a baya na kamar ta kaho.
11 wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”
Ta ce, “Rubuta abinda ka gani a cikin littafi, ka kuma aika wa ikilisiyoyin nan bakwai - ga Afisus, ga Simirna, ga Birgamas, ga Tayatira, ga Sardisu, ga Filadalfiya, da kuma ga Laudikiya.”
12 Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya.
Na juya don in ga wanda muryarsa ke magana da ni, da na juya sai na ga fitilu bakwai akan madorin su
13 A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa.
A tsakiyar fitilun akwai wani mai kama da dan mutum, yana sanye da doguwar tufa har tafin sawunsa, da damara ta zinariya kewaye a kirjinsa.
14 Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta.
Kansa da gashinsa fari fat kamar auduga - kamar dusar kankara, kuma idanun sa kamar harshen wuta.
15 Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu.
Kafaffunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar tagullar da aka tace da wutar makera, muryar sa kuma kamar kugin ambaliyar ruwan teku ne.
16 A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
A hannunsa na dama yana rike da taurari bakwai, daga bakinsa kuma kakkaifan takobi mai kaifi biyu ke fitowa. Fuskarsa tana haskakawa kamar sa'adda rana ke haskakawa kwarai.
17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe.
Lokacin da na gan shi, na fadi kamar mataccen mutum a kafaffunsa. Ya dora hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Nine na farko da na karshe,
18 Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades. (aiōn , Hadēs )
da kuma wanda ke raye. Na mutu, amma duba ina raye har abada! Kuma ina da mabudin mutuwa da na hades. (aiōn , Hadēs )
19 “Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba.
Domin haka ka rubuta abinda ka gani, abin da ke yanzu, da abin da zai faru bayan wanan.
20 Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne.
Akan boyayyar ma'ana game da taurari bakwai da ka gani a hannun dama na, da madorin fitilu bakwai na zinariya: Taurarin nan bakwai mala'iku ne na ikilisiyoyi bakwai, kuma madorin fitilun nan bakwai ikilisiyoyi ne bakwai.