< Zabura 1 >
1 Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
Blessed is the man who does not walk in the counsel of the wicked, or set foot on the path of sinners, or sit in the seat of mockers.
2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.
But his delight is in the Law of the LORD, and on His law he meditates day and night.
3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
He is like a tree planted by streams of water, yielding its fruit in season, whose leaf does not wither, and who prospers in all he does.
4 Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.
Not so the wicked! For they are like chaff driven off by the wind.
5 Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.
Therefore the wicked will not stand in the judgment, nor sinners in the assembly of the righteous.
6 Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.
For the LORD guards the path of the righteous, but the way of the wicked will perish.