< Zabura 97 >

1 Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.
יהוה מלך תגל הארץ ישמחו איים רבים
2 Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.
ענן וערפל סביביו צדק ומשפט מכון כסאו
3 Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.
אש לפניו תלך ותלהט סביב צריו
4 Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.
האירו ברקיו תבל ראתה ותחל הארץ
5 Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.
הרים--כדונג נמסו מלפני יהוה מלפני אדון כל-הארץ
6 Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.
הגידו השמים צדקו וראו כל-העמים כבודו
7 Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli!
יבשו כל-עבדי פסל-- המתהללים באלילים השתחוו-לו כל-אלהים
8 Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.
שמעה ותשמח ציון ותגלנה בנות יהודה-- למען משפטיך יהוה
9 Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli.
כי-אתה יהוה עליון על-כל-הארץ מאד נעלית על-כל-אלהים
10 Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
אהבי יהוה שנאו-רע שמר נפשות חסידיו מיד רשעים יצילם
11 An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.
אור זרע לצדיק ולישרי-לב שמחה
12 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki.
שמחו צדיקים ביהוה והודו לזכר קדשו

< Zabura 97 >