< Zabura 95 >

1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu. 2 Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa. 3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli. 4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne. 5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. 6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu; 7 gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa, 8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada, 9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi. 10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’ 11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’”

< Zabura 95 >