< Zabura 95 >
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli.
4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.
6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
7 gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,
8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,
9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.
10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’
11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’”