< Zabura 94 >

1 Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.
אל-נקמות יהוה אל נקמות הופיע
2 Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.
הנשא שפט הארץ השב גמול על-גאים
3 Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna?
עד-מתי רשעים יהוה עד-מתי רשעים יעלזו
4 Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.
יביעו ידברו עתק יתאמרו כל-פעלי און
5 Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka.
עמך יהוה ידכאו ונחלתך יענו
6 Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu.
אלמנה וגר יהרגו ויתומים ירצחו
7 Suna ce, “Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.”
ויאמרו לא יראה-יה ולא-יבין אלהי יעקב
8 Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
בינו בערים בעם וכסילים מתי תשכילו
9 Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
הנטע אזן הלא ישמע אם-יצר עין הלא יביט
10 Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
היסר גוים הלא יוכיח המלמד אדם דעת
11 Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.
יהוה--ידע מחשבות אדם כי-המה הבל
12 Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;
אשרי הגבר אשר-תיסרנו יה ומתורתך תלמדנו
13 kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye.
להשקיט לו מימי רע-- עד יכרה לרשע שחת
14 Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba.
כי לא-יטש יהוה עמו ונחלתו לא יעזב
15 Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.
כי-עד-צדק ישוב משפט ואחריו כל-ישרי-לב
16 Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?
מי-יקום לי עם-מרעים מי-יתיצב לי עם-פעלי און
17 Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
לולי יהוה עזרתה לי-- כמעט שכנה דומה נפשי
18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.
אם-אמרתי מטה רגלי חסדך יהוה יסעדני
19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
ברב שרעפי בקרבי-- תנחומיך ישעשעו נפשי
20 Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?
היחברך כסא הוות יצר עמל עלי-חק
21 Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.
יגודו על-נפש צדיק ודם נקי ירשיעו
22 Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.
ויהי יהוה לי למשגב ואלהי לצור מחסי
23 Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.
וישב עליהם את אונם-- וברעתם יצמיתם יצמיתם יהוה אלהינו

< Zabura 94 >