< Zabura 93 >
1 Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
上主為王,以尊威作衣冠;上主身著德能,腰束大權。上主奠定了大地塵寰,大地塵寰不再搖撼;
2 An kafa kursiyin tun da daɗewa; kana nan tun fil azal.
您的寶座由太初即已建立,您的存在,從恆古即已開始。
3 Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.
上主,江河已經揚波,江河已經澎湃怒號,江河已經似雷狂嘯。
4 Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.
高天的上主具有大能,壓倒滔滔洪水巨聲,沖散汪洋大海波峰。
5 Ƙa’idodinka suna nan daram; tsarki ya yi wa gidanka ado har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.
上主,您的約言萬分忠實可信,您的殿宇永遠應享神聖。