< Zabura 92 >
1 Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2 don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,
3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.
4 Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
5 Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
6 Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,
7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.
8 Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.
9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.
11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.
12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
13 da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
14 Za su ci gaba da ba da’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,
15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”