< Zabura 91 >

1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
He who lives in the shelter of the Most High will stay in the shadow of the Almighty.
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.”
I will say of Yahweh, “He is my refuge and my fortress, my God, in whom I trust.”
3 Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa.
For he will rescue you from the snare of the hunter and from the deadly plague.
4 Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
He will cover you with his wings, and under his wings you will find refuge. His trustworthiness is a shield and protection.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
You will not be afraid of terror in the night, or of the arrow that flies by day,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
or of the plague that roams around in the darkness, or of the disease that comes at noontime.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.
A thousand may fall at your side and ten thousand at your right hand, but it will not reach you.
8 Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye.
You will only observe and see the punishment of the wicked.
9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
For Yahweh is my refuge! Make the Most High your refuge also.
10 to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
No evil will overtake you; no affliction will come near your home.
11 Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
For he will direct his angels to protect you, to guard you in all your ways.
12 za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
They will lift you up with their hand so that you will not hit your foot on a stone.
13 Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji.
You will crush lions and adders under your feet; you will trample on young lions and serpents.
14 Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.
Because he is devoted to me, I will rescue him. I will protect him because he is loyal to me.
15 Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
When he calls to me, I will answer him. I will be with him in trouble; I will give him victory and will honor him.
16 Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”
I will satisfy him with long life and show him my salvation.

< Zabura 91 >