< Zabura 90 >

1 Addu’ar Musa Mutumin Allah. Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai.
תפלה למשה איש-האלהים אדני--מעון אתה היית לנו בדר ודר
2 Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.
בטרם הרים ילדו-- ותחולל ארץ ותבל ומעולם עד-עולם אתה אל
3 Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku’ya’yan mutane.”
תשב אנוש עד-דכא ותאמר שובו בני-אדם
4 Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare.
כי אלף שנים בעיניך-- כיום אתמול כי יעבר ואשמורה בלילה
5 Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya,
זרמתם שנה יהיו בבקר כחציר יחלף
6 ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.
בבקר יציץ וחלף לערב ימולל ויבש
7 An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka.
כי-כלינו באפך ובחמתך נבהלנו
8 Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.
שת (שתה) עונתינו לנגדך עלמנו למאור פניך
9 Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi.
כי כל-ימינו פנו בעברתך כלינו שנינו כמו-הגה
10 Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.
ימי-שנותינו בהם שבעים שנה ואם בגבורת שמונים שנה-- ורהבם עמל ואון כי-גז חיש ונעפה
11 Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai.
מי-יודע עז אפך וכיראתך עברתך
12 Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima.
למנות ימינו כן הודע ונבא לבב חכמה
13 Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka.
שובה יהוה עד-מתי והנחם על-עבדיך
14 Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.
שבענו בבקר חסדך ונרננה ונשמחה בכל-ימינו
15 Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala.
שמחנו כימות עניתנו שנות ראינו רעה
16 Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga’ya’yansu.
יראה אל-עבדיך פעלך והדרך על-בניהם
17 Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.
ויהי נעם אדני אלהינו-- עלינו ומעשה ידינו כוננה עלינו ומעשה ידינו כוננהו

< Zabura 90 >