< Zabura 9 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
To the Overseer, 'On the Death of Labben.' — A Psalm of David. I confess, O Jehovah, with all my heart, I recount all Thy wonders,
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka; zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
I rejoice and exult in Thee, I praise Thy Name, O Most High.
3 Abokan gābana sun ja da baya; suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
In mine enemies turning backward, they stumble and perish from Thy face.
4 Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi; ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
For Thou hast done my judgment and my right. Thou hast sat on a throne, A judge of righteousness.
5 Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye; ka shafe sunansu har abada abadin.
Thou hast rebuked nations, Thou hast destroyed the wicked, Their name Thou hast blotted out to the age and for ever.
6 Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu, ka tuttumɓuke biranensu; yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
O thou Enemy, Finished have been destructions for ever, As to cities thou hast plucked up, Perished hath their memorial with them.
7 Ubangiji yana mulki har abada; ya kafa kujerarsa don shari’a.
And Jehovah to the age abideth, He is preparing for judgment His throne.
8 Zai hukunta duniya da adalci; zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
And He judgeth the world in righteousness, He judgeth the peoples in uprightness.
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala.
And Jehovah is a tower for the bruised, A tower for times of adversity.
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
They trust in Thee who do know Thy name, For Thou hast not forsaken Those seeking Thee, O Jehovah.
11 Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
Sing ye praise to Jehovah, inhabiting Zion, Declare ye among the peoples His acts,
12 Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.
For He who is seeking for blood Them hath remembered, He hath not forgotten the cry of the afflicted.
13 Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
Favour me, O Jehovah, See mine affliction by those hating me, Thou who liftest me up from the gates of death,
14 don in furta yabanka cikin ƙofofin’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
So that I recount all Thy praise, In the gates of the daughter of Zion. I rejoice on Thy salvation.
15 Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu; aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.
Sunk have nations in a pit they made, In a net that they hid hath their foot been captured.
16 An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa; an kama mugaye da aikin hannuwansu. Haggayiyon. (Sela)
Jehovah hath been known, Judgment He hath done, By a work of his hands Hath the wicked been snared. (Meditation, Selah)
17 Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. (Sheol h7585)
The wicked do turn back to Sheol, All nations forgetting God. (Sheol h7585)
18 Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
For not for ever is the needy forgotten, The hope of the humble lost to the age.
19 Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka.
Rise, O Jehovah, let not man be strong, Let nations be judged before Thy face.
20 Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. (Sela)
Appoint, O Jehovah, a director to them, Let nations know they [are] men! (Selah)

< Zabura 9 >