< Zabura 87 >

1 Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki.
コラの子の歌、さんび 主が基をすえられた都は聖なる山の上に立つ。
2 Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.
主はヤコブのすべてのすまいにまさって、シオンのもろもろの門を愛される。
3 Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, (Sela)
神の都よ、あなたについて、もろもろの栄光ある事が語られる。 (セラ)
4 “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’”
わたしはラハブとバビロンをわたしを知る者のうちに挙げる。ペリシテ、ツロ、またエチオピヤを見よ。「この者はかしこに生れた」と言われる。
5 Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”
しかしシオンについては「この者も、かの者もその中に生れた」と言われる。いと高き者みずからシオンを堅く立てられるからである。
6 Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” (Sela)
主がもろもろの民を登録されるとき、「この者はかしこに生れた」としるされる。 (セラ)
7 Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”
歌う者と踊る者はみな言う、「わがもろもろの泉はあなたのうちにある」と。

< Zabura 87 >