< Zabura 86 >
1 Addu’ar Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma.
A prayer of David. Incline Your ear, O LORD, and answer me, for I am poor and needy.
2 Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka.
Preserve my soul, for I am godly. You are my God; save Your servant who trusts in You.
3 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini.
Be merciful to me, O Lord, for I call to You all day long.
4 Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina.
Bring joy to Your servant, for to You, O Lord, I lift up my soul.
5 Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.
For You, O Lord, are kind and forgiving, rich in loving devotion to all who call on You.
6 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai.
Hear my prayer, O LORD, and attend to my plea for mercy.
7 A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini.
In the day of my distress I call on You, because You answer me.
8 A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji; babu ayyukan da za a kwatanta da naka.
O Lord, there is none like You among the gods, nor any works like Yours.
9 Dukan al’umman da ka yi za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji; za su kawo ɗaukaka ga sunanka.
All the nations You have made will come and bow before You, O Lord, and they will glorify Your name.
10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki; kai kaɗai ne Allah.
For You are great and perform wonders; You alone are God.
11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji, zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka; ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba, don in ji tsoron sunanka.
Teach me Your way, O LORD, that I may walk in Your truth. Give me an undivided heart, that I may fear Your name.
12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada.
I will praise You, O Lord my God, with all my heart; I will glorify Your name forever.
13 Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu. (Sheol )
For great is Your loving devotion to me; You have delivered me from the depths of Sheol. (Sheol )
14 Masu girman kai suna kai mini hari, ya Allah; ƙungiyar marasa imani suna neman raina, mutanen da ba su kula da kai ba.
The arrogant rise against me, O God; a band of ruthless men seeks my life, with no regard for You.
15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.
But You, O Lord, are a compassionate and gracious God, slow to anger, abounding in loving devotion and faithfulness.
16 Ka juyo gare ni ka yi mini jinƙai; ka ba wa bawanka ƙarfi; ka ceci ni gama na bauta maka yadda mahaifiyata ta yi.
Turn to me and have mercy; grant Your strength to Your servant; save the son of Your maidservant.
17 Ka ba ni alamar alherinka, don abokan gābana su gani su kuma sha kunya, gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni.
Show me a sign of Your goodness, that my enemies may see and be ashamed; for You, O LORD, have helped me and comforted me.