< Zabura 84 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!
[For the Chief Musician. On an instrument of Gath. A Psalm by the sons of Korah.] How lovely are your dwellings, LORD of hosts.
2 Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.
My soul longs, yes, yearns for the courts of the LORD. My heart and my flesh cry out for the living God.
3 Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.
Yes, the sparrow has found a home, and the swallow a nest for herself, where she may have her young, near your altars, LORD of hosts, my King, and my God.
4 Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. (Sela)
Blessed are those who dwell in your house. They are ever praising you. (Selah)
5 Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.
Blessed are those whose strength is in you, who have set their hearts on a pilgrimage.
6 Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.
Passing through the Valley of Baca, he makes it into a spring. Yes, the autumn rain covers it with blessings.
7 Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.
They go from strength to strength. Everyone of them appears before God in Zion.
8 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. (Sela)
LORD, God of hosts, hear my prayer. Listen, God of Jacob. (Selah)
9 Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka.
Look, God our shield, look at the face of your anointed.
10 Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye.
For a day in your courts is better than a thousand. I would rather be a doorkeeper in the house of God, than to dwell in the tents of wickedness.
11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
For the LORD God is a sun and a shield. The LORD will give grace and glory. He withholds no good thing from those who walk blamelessly.
12 Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.
LORD of hosts, blessed is the man who trusts in you.

< Zabura 84 >