< Zabura 83 >

1 Waƙa ce. Zabura ta Asaf. Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi.
שיר מזמור לאסף ב אלהים אל-דמי-לך אל-תחרש ואל-תשקט אל
2 Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.
כי-הנה אויביך יהמיון ומשנאיך נשאו ראש
3 Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.
על-עמך יערימו סוד ויתיעצו על-צפוניך
4 Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”
אמרו--לכו ונכחידם מגוי ולא-יזכר שם-ישראל עוד
5 Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai,
כי נועצו לב יחדו עליך ברית יכרתו
6 tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa,
אהלי אדום וישמעאלים מואב והגרים
7 Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya.
גבל ועמון ועמלק פלשת עם-ישבי צור
8 Har Assuriya ma ta haɗa kai da su don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. (Sela)
גם-אשור נלוה עמם היו זרוע לבני-לוט סלה
9 Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,
עשה-להם כמדין כסיסרא כיבין בנחל קישון
10 waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa.
נשמדו בעין-דאר היו דמן לאדמה
11 Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,
שיתמו נדיבימו כערב וכזאב וכזבח וכצלמנע כל-נסיכימו
12 waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.”
אשר אמרו נירשה לנו-- את נאות אלהים
13 Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa,
אלהי שיתמו כגלגל כקש לפני-רוח
14 kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,
כאש תבער-יער וכלהבה תלהט הרים
15 haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka.
כן תרדפם בסערך ובסופתך תבהלם
16 Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.
מלא פניהם קלון ויבקשו שמך יהוה
17 Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci.
יבשו ויבהלו עדי-עד ויחפרו ויאבדו
18 Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.
וידעו-- כי-אתה שמך יהוה לבדך עליון על-כל-הארץ

< Zabura 83 >