< Zabura 82 >

1 Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.
מזמור לאסף אלהים נצב בעדת-אל בקרב אלהים ישפט
2 “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? (Sela)
עד-מתי תשפטו-עול ופני רשעים תשאו-סלה
3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
שפטו-דל ויתום עני ורש הצדיקו
4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
פלטו-דל ואביון מיד רשעים הצילו
5 “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.
לא ידעו ולא יבינו-- בחשכה יתהלכו ימוטו כל-מוסדי ארץ
6 “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.
אני-אמרתי אלהים אתם ובני עליון כלכם
7 Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”
אכן כאדם תמותון וכאחד השרים תפלו
8 Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.
קומה אלהים שפטה הארץ כי-אתה תנחל בכל-הגוים

< Zabura 82 >