< Zabura 81 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!
לַמְנַצֵּחַ ׀ עַֽל־הַגִּתִּית לְאָסָֽף׃ הַרְנִינוּ לֵאלֹהִים עוּזֵּנוּ הָרִיעוּ לֵאלֹהֵי יַעֲקֹֽב׃
2 Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
שְֽׂאוּ־זִמְרָה וּתְנוּ־תֹף כִּנּוֹר נָעִים עִם־נָֽבֶל׃
3 Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;
תִּקְעוּ בַחֹדֶשׁ שׁוֹפָר בַּכֵּסֶה לְיוֹם חַגֵּֽנוּ׃
4 wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub.
כִּי חֹק לְיִשְׂרָאֵל הוּא מִשְׁפָּט לֵאלֹהֵי יַעֲקֹֽב׃
5 Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.
עֵדוּת ׀ בִּיהוֹסֵף שָׂמוֹ בְּצֵאתוֹ עַל־אֶרֶץ מִצְרָיִם שְׂפַת לֹא־יָדַעְתִּי אֶשְׁמָֽע׃
6 Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an’yantar da hannuwansu daga kwando.
הֲסִירוֹתִי מִסֵּבֶל שִׁכְמוֹ כַּפָּיו מִדּוּד תַּעֲבֹֽרְנָה׃
7 Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. (Sela)
בַּצָּרָה קָרָאתָ וָאֲחַלְּצֶךָּ אֶעֶנְךָ בְּסֵתֶר רַעַם אֶבְחׇנְךָ עַל־מֵי מְרִיבָה סֶֽלָה׃
8 “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!
שְׁמַע עַמִּי וְאָעִידָה בָּךְ יִשְׂרָאֵל אִם־תִּֽשְׁמַֽע־לִֽי׃
9 Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.
לֹא־יִהְיֶה בְךָ אֵל זָר וְלֹא תִשְׁתַּחֲוֶה לְאֵל נֵכָֽר׃
10 Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
אָֽנֹכִי ׀ יְהֹוָה אֱלֹהֶיךָ הַֽמַּעַלְךָ מֵאֶרֶץ מִצְרָיִם הַרְחֶב־פִּיךָ וַאֲמַלְאֵֽהוּ׃
11 “Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.
וְלֹֽא־שָׁמַע עַמִּי לְקוֹלִי וְיִשְׂרָאֵל לֹא־אָבָה לִֽי׃
12 Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu.
וָאֲשַׁלְּחֵהוּ בִּשְׁרִירוּת לִבָּם יֵלְכוּ בְּֽמוֹעֲצוֹתֵיהֶֽם׃
13 “A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,
לוּ עַמִּי שֹׁמֵעַֽ לִי יִשְׂרָאֵל בִּדְרָכַי יְהַלֵּֽכוּ׃
14 da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!
כִּמְעַט אוֹיְבֵיהֶם אַכְנִיעַ וְעַל צָרֵיהֶם אָשִׁיב יָדִֽי׃
15 Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.
מְשַׂנְאֵי יְהֹוָה יְכַחֲשׁוּ־לוֹ וִיהִי עִתָּם לְעוֹלָֽם׃
16 Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”
וַֽיַּאֲכִילֵהוּ מֵחֵלֶב חִטָּה וּמִצּוּר דְּבַשׁ אַשְׂבִּיעֶֽךָ׃

< Zabura 81 >