< Zabura 80 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka
[For the Chief Musician. To the tune of "The Lilies of the Covenant." A Psalm by Asaph.] Hear us, Shepherd of Israel, you who lead Joseph like a flock, you who sit above the cherubim, shine forth.
2 a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu.
Before Ephraim and Benjamin and Manasseh, stir up your might. Come to save us.
3 Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.
Restore us, God. Cause your face to shine, and we will be saved.
4 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka?
LORD God of hosts, How long will you be angry against the prayer of your people?
5 Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.
You have fed them with the bread of tears, and given them tears to drink in large measure.
6 Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.
You make us a source of contention to our neighbors. Our enemies have mocked us.
7 Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.
Restore us, God of hosts. Cause your face to shine, and we will be saved.
8 Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.
You brought a vine out of Egypt. You drove out the nations, and planted it.
9 Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.
You cleared the ground for it. It took deep root, and filled the land.
10 Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.
The mountains were covered with its shadow. Its boughs were like God's cedars.
11 Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.
It sent out its branches to the sea, Its shoots to the River.
12 Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke’ya’yan inabinsa?
Why have you broken down its walls, so that all those who pass by the way pluck it?
13 Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.
The boar out of the wood ravages it. The wild animals of the field feed on it.
14 Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,
Return, we beg you, God of hosts. Look down from heaven, and see, and visit this vine,
15 saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.
the stock which your right hand planted, the branch that you made strong for yourself.
16 An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.
It's burned with fire. It's cut down. They perish at your rebuke.
17 Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka.
Let your hand be on the man of your right hand, on the son of man whom you made strong for yourself.
18 Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.
So we will not turn away from you. Revive us, and we will call on your name.
19 Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.
Restore us, LORD God of hosts. Cause your face to shine, and we will be saved.

< Zabura 80 >