< Zabura 79 >

1 Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.
מזמור לאסף אלהים באו גוים בנחלתך-- טמאו את היכל קדשך שמו את-ירושלם לעיים
2 Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.
נתנו את-נבלת עבדיך-- מאכל לעוף השמים בשר חסידיך לחיתו-ארץ
3 Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu.
שפכו דמם כמים--סביבות ירושלם ואין קובר
4 Mun zama abin reni ga maƙwabta, abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
היינו חרפה לשכנינו לעג וקלס לסביבותינו
5 Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?
עד-מה יהוה תאנף לנצח תבער כמו-אש קנאתך
6 Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka;
שפך חמתך-- אל הגוים אשר לא-ידעוך ועל ממלכות-- אשר בשמך לא קראו
7 gama sun cinye Yaƙub suka lalatar da ƙasar zamansa.
כי אכל את-יעקב ואת-נוהו השמו
8 Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai.
אל-תזכר-לנו עונת ראשנים מהר יקדמונו רחמיך-- כי דלונו מאד
9 Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka.
עזרנו אלהי ישענו-- על-דבר כבוד-שמך והצילנו וכפר על-חטאתינו למען שמך
10 Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.
למה יאמרו הגוים-- איה אלהיהם יודע בגיים (בגוים) לעינינו נקמת דם-עבדיך השפוך
11 Bari nishe-nishen’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.
תבוא לפניך אנקת אסיר כגדל זרועך--הותר בני תמותה
12 Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.
והשב לשכנינו שבעתים אל-חיקם חרפתם אשר חרפוך אדני
13 Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka.
ואנחנו עמך וצאן מרעיתך-- נודה לך לעולם לדר ודר-- נספר תהלתך

< Zabura 79 >