< Zabura 77 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Na Asaf. Zabura ce. Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni.
2 Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.
3 Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. (Sela)
4 ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana.
5 Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa;
6 na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.
7 “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?
8 Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?
9 Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” (Sela)
10 Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”
11 Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.
12 Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.
13 Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?
14 Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane.
15 Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. (Sela)
16 Ruwaye sun gan ka, ya Allah, ruwaye sun gan ka suka firgita; zurfafan gaske sun girgiza.
17 Gizagizai sun sauko da ruwa, sararin sama suka buga tsawa; kibiyoyinka suka yi ta kai komo da walƙiya.
18 Aka ji tsawanka a cikin guguwa, walƙiyarka ta haskaka duniya; duniya ta yi rawar jiki ta girgiza.
19 Hanyarka ta bi ta cikin teku, hanyarka ta bi cikin manyan ruwaye, duk da haka ba a ga sawunka ba.
20 Ka bi da mutanenka kamar garke ta hannun Musa da Haruna.