< Zabura 76 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
For the Leader; with string-music. A Psalm of Asaph, a Song. In Judah is God known; His name is great in Israel.
2 Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
In Salem also is set His tabernacle, and His dwelling-place in Zion.
3 A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. (Sela)
There He broke the fiery shafts of the bow; the shield, and the sword, and the battle. (Selah)
4 Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
Glorious art Thou and excellent, coming down from the mountains of prey.
5 Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.
The stout-hearted are bereft of sense, they sleep their sleep; and none of the men of might have found their hands.
6 A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
At Thy rebuke, O God of Jacob, they are cast into a dead sleep, the riders also and the horses.
7 Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
Thou, even Thou, art terrible; and who may stand in Thy sight when once Thou art angry?
8 Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
Thou didst cause sentence to be heard from heaven; the earth feared, and was still,
9 sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. (Sela)
When God arose to judgment, to save all the humble of the earth. (Selah)
10 Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
Surely the wrath of man shall praise Thee; the residue of wrath shalt Thou gird upon Thee.
11 Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
Vow, and pay unto the LORD your God; let all that are round about Him bring presents unto Him that is to be feared;
12 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.
He minisheth the spirit of princes; He is terrible to the kings of the earth.

< Zabura 76 >