< Zabura 74 >

1 Maskil na Asaf. Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?
משכיל לאסף למה אלהים זנחת לנצח יעשן אפך בצאן מרעיתך
2 Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa, kabilar gādonka, wadda ka fansa, Dutsen Sihiyona, inda ka zauna.
זכר עדתך קנית קדם-- גאלת שבט נחלתך הר-ציון זה שכנת בו
3 Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai, dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki.
הרימה פעמיך למשאות נצח כל-הרע אויב בקדש
4 Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu; suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu.
שאגו צרריך בקרב מועדך שמו אותתם אתות
5 Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi.
יודע כמביא למעלה בסבך-עץ קרדמות
6 Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu.
ועת (ועתה) פתוחיה יחד-- בכשיל וכילפות יהלמון
7 Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus; suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.
שלחו באש מקדשך לארץ חללו משכן-שמך
8 Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!” Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar.
אמרו בלבם נינם יחד שרפו כל-מועדי-אל בארץ
9 Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.
אותתינו לא ראינו אין-עוד נביא ולא-אתנו ידע עד-מה
10 Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?
עד-מתי אלהים יחרף צר ינאץ אויב שמך לנצח
11 Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su!
למה תשיב ידך וימינך מקרב חוקך (חיקך) כלה
12 Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya.
ואלהים מלכי מקדם פעל ישועות בקרב הארץ
13 Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka; ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.
אתה פוררת בעזך ים שברת ראשי תנינים על-המים
14 Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.
אתה רצצת ראשי לויתן תתננו מאכל לעם לציים
15 Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka; ka busar da koguna masu ruwa.
אתה בקעת מעין ונחל אתה הובשת נהרות איתן
16 Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata.
לך יום אף-לך לילה אתה הכינות מאור ושמש
17 Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina.
אתה הצבת כל-גבולות ארץ קיץ וחרף אתה יצרתם
18 Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji, yadda wawaye suka ɓata sunanka.
זכר-זאת--אויב חרף יהוה ועם נבל נאצו שמך
19 Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji; kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.
אל-תתן לחית נפש תורך חית ענייך אל-תשכח לנצח
20 Ka kula da alkawarinka, domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.
הבט לברית כי מלאו מחשכי-ארץ נאות חמס
21 Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya; bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.
אל-ישב דך נכלם עני ואביון יהללו שמך
22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka; ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.
קומה אלהים ריבה ריבך זכר חרפתך מני-נבל כל-היום
23 Kada ka ƙyale surutan ban haushi na maƙiyanka, ihun abokan gābanka, waɗanda suke ci gaba da yi.
אל-תשכח קול צרריך שאון קמיך עלה תמיד

< Zabura 74 >