< Zabura 73 >
1 Zabura ta Asaf. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.
2 Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.
3 Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.
4 Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.
5 Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na’yan adam.
6 Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.
7 Daga mugayen zukatansu laifi kan fito mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.
8 Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa; cikin girman kan suna barazana yin danniya.
9 Bakunansu na cewa sama na su ne, kuma harsunansu sun mallaki duniya.
10 Saboda haka mutanensu sun juya gare su suna kuma shan ruwa a yalwace.
11 Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”
12 Ga yadda mugaye suke, kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.
13 Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta; a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.
14 Dukan yini na sha annoba; an hukunta ni kowace safiya.
15 Da na ce, “Zan faɗa haka,” da na bashe’ya’yanka.
16 Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan, sai ya zama danniya a gare ni
17 sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.
18 Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.
19 Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!
20 Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.
21 Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,
22 na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.
23 Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana.
24 Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.
25 Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.
26 Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.
27 Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci.
28 Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka.