< Zabura 72 >

1 Ta Solomon. Ka tanada sarki da shari’arka ta gaskiya, ya Allah, ɗan sarki da adalcinka.
לשלמה אלהים--משפטיך למלך תן וצדקתך לבן-מלך
2 Zai shari’anta mutanenka da adalci, marasa ƙarfinka da shari’ar gaskiya.
ידין עמך בצדק וענייך במשפט
3 Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.
ישאו הרים שלום לעם וגבעות בצדקה
4 Zai kāre marasa ƙarfi a cikin mutane yă kuma cece’ya’yan masu bukata; zai murƙushe masu danniya.
ישפט עניי-עם--יושיע לבני אביון וידכא עושק
5 Zai jimre muddin rana tana nan, muddin akwai wata, har dukan zamanai.
ייראוך עם-שמש ולפני ירח דור דורים
6 Zai zama kamar ruwan sama mai fāɗuwa a filin ciyayin da aka yanka, kamar yayyafi mai ba wa duniya ruwa.
ירד כמטר על-גז כרביבים זרזיף ארץ
7 A kwanakinsa adalai za su haɓaka wadata za tă yalwata har sai babu sauran wata.
יפרח-בימיו צדיק ורב שלום עד-בלי ירח
8 Zai yi mulki daga teku zuwa teku kuma daga Kogi zuwa iyakar duniya.
וירד מים עד-ים ומנהר עד-אפסי-ארץ
9 Kabilun hamada za su rusuna a gabansa abokan gābansa kuwa za su lashe ƙura.
לפניו יכרעו ציים ואיביו עפר ילחכו
10 Sarakunan Tarshish da na bakin kogi masu nisa za su ba da gandu gare shi; sarakunan Sheba da Seba za su ba shi kyautai.
מלכי תרשיש ואיים מנחה ישיבו מלכי שבא וסבא אשכר יקריבו
11 Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.
וישתחוו-לו כל-מלכים כל-גוים יעבדוהו
12 Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako.
כי-יציל אביון משוע ועני ואין-עזר לו
13 Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.
יחס על-דל ואביון ונפשות אביונים יושיע
14 Zai kuɓutar da su daga danniya da rikici, gama jininsu yake a gabansa.
מתוך ומחמס יגאל נפשם וייקר דמם בעיניו
15 Bari yă yi doguwar rayuwa! Bari a ba shi zinariya daga Sheba. Bari mutane su riƙa yin addu’a dominsa su kuma albarkace shi dukan yini.
ויחי-- ויתן-לו מזהב שבא ויתפלל בעדו תמיד כל-היום יברכנהו
16 Bari hatsi yă yalwata a duk fāɗin ƙasar; bari yă cika bisan tuddai. Bari’ya’yan itatuwansa su haɓaka kamar Lebanon; bari yă bazu kamar ciyayi a gona.
יהי פסת-בר בארץ-- בראש הרים ירעש כלבנון פריו ויציצו מעיר כעשב הארץ
17 Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.
יהי שמו לעולם-- לפני-שמש ינין (ינון) שמו ויתברכו בו כל-גוים יאשרוהו
18 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.
ברוך יהוה אלהים--אלהי ישראל עשה נפלאות לבדו
19 Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa.
וברוך שם כבודו-- לעולם וימלא כבודו את-כל הארץ-- אמן ואמן
20 Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.
כלו תפלות-- דוד בן-ישי

< Zabura 72 >