< Zabura 71 >

1 A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka taɓa sa in sha kunya.
בך-יהוה חסיתי אל-אבושה לעולם
2 Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka; ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni.
בצדקתך תצילני ותפלטני הטה-אלי אזנך והושיעני
3 Ka zama dutsena da kagarata, inda kullum zan je. Ka ba da umarni a cece ni, gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata.
היה לי לצור מעון לבוא-- תמיד צוית להושיעני כי-סלעי ומצודתי אתה
4 Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye, da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.
אלהי--פלטני מיד רשע מכף מעול וחומץ
5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
כי-אתה תקותי אדני יהוה מבטחי מנעורי
6 Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka.
עליך נסמכתי מבטן--ממעי אמי אתה גוזי בך תהלתי תמיד
7 Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi.
כמופת הייתי לרבים ואתה מחסי-עז
8 Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini.
ימלא פי תהלתך כל-היום תפארתך
9 Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa; kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare.
אל-תשליכני לעת זקנה ככלות כחי אל-תעזבני
10 Gama abokan gābana suna magana a kaina; waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare.
כי-אמרו אויבי לי ושמרי נפשי נועצו יחדו
11 Suna cewa, “Allah ya yashe shi; mu fafare shi mu kama shi, gama ba wanda zai kuɓutar da shi.”
לאמר אלהים עזבו רדפו ותפשוהו כי-אין מציל
12 Kada ka yi nisa da ni, ya Allah; zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni.
אלהים אל-תרחק ממני אלהי לעזרתי חישה (חושה)
13 Bari masu zagina su hallaka da kunya; bari waɗanda suke so su cutar da ni su sha ba’a da kuma kunya.
יבשו יכלו שטני נפשי יעטו חרפה וכלמה--מבקשי רעתי
14 Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau.
ואני תמיד איחל והוספתי על-כל-תהלתך
15 Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba.
פי יספר צדקתך--כל-היום תשועתך כי לא ידעתי ספרות
16 Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.
אבוא--בגברות אדני יהוה אזכיר צדקתך לבדך
17 Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.
אלהים למדתני מנעורי ועד-הנה אגיד נפלאותיך
18 Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.
וגם עד-זקנה ושיבה-- אלהים אל-תעזבני עד-אגיד זרועך לדור לכל-יבוא גבורתך
19 Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah?
וצדקתך אלהים עד-מרום אשר-עשית גדלות אלהים מי כמוך
20 Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni.
אשר הראיתנו (הראיתני) צרות רבות-- ורעות תשוב תחינו (תחיני) ומתהמות הארץ תשוב תעלני
21 Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni.
תרב גדלתי ותסב תנחמני
22 Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
גם-אני אודך בכלי-נבל-- אמתך אלהי אזמרה לך בכנור-- קדוש ישראל
23 Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa.
תרננה שפתי כי אזמרה-לך ונפשי אשר פדית
24 Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice.
גם-לשוני-- כל-היום תהגה צדקתך כי-בשו כי-חפרו מבקשי רעתי

< Zabura 71 >