< Zabura 70 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo. Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.
大衛的紀念詩,交與伶長。 上帝啊,求你快快搭救我! 耶和華啊,求你速速幫助我!
2 Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan masu sha’awar gani lalacewata su juye baya da kunya.
願那些尋索我命的,抱愧蒙羞; 願那些喜悅我遭害的,退後受辱。
3 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu.
願那些對我說阿哈、阿哈的, 因羞愧退後。
4 Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”
願一切尋求你的,因你高興歡喜; 願那些喜愛你救恩的,常說:當尊上帝為大!
5 Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.
但我是困苦窮乏的; 上帝啊,求你速速到我這裏來! 你是幫助我的,搭救我的。 耶和華啊,求你不要耽延!

< Zabura 70 >