< Zabura 7 >
1 Wani shiggayiyon ta Dawuda, wanda Ya Rera wa Ubangiji game da Kush mutumin Benyamin. Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,
2 in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba.
3 Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana,
4 in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,
5 to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. (Sela)
6 Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci.
7 Bari taron mutane su taru kewaye da kai. Ka yi mulki a bisansu daga bisa;
8 bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.
9 Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya.
10 Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya.
11 Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.
12 In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa.
13 Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.
14 Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya.
15 Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa.
16 Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa.
17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.