< Zabura 69 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata
למנצח על-שושנים לדוד ב הושיעני אלהים-- כי באו מים עד-נפש
2 Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.
טבעתי ביון מצולה-- ואין מעמד באתי במעמקי-מים ושבלת שטפתני
3 Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.
יגעתי בקראי נחר גרוני כלו עיני--מיחל לאלהי
4 Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba.
רבו משערות ראשי-- שנאי חנם עצמו מצמיתי איבי שקר-- אשר לא-גזלתי אז אשיב
5 Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
אלהים--אתה ידעת לאולתי ואשמותי ממך לא-נכחדו
6 Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.
אל-יבשו בי קויך-- אדני יהוה צבאות אל-יכלמו בי מבקשיך-- אלהי ישראל
7 Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.
כי-עליך נשאתי חרפה כסתה כלמה פני
8 Ni baƙo ne a cikin’yan’uwana, bare kuma ga’ya’yan mahaifiyata maza;
מוזר הייתי לאחי ונכרי לבני אמי
9 gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.
כי-קנאת ביתך אכלתני וחרפות חורפיך נפלו עלי
10 Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a;
ואבכה בצום נפשי ותהי לחרפות לי
11 sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.
ואתנה לבושי שק ואהי להם למשל
12 Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.
ישיחו בי ישבי שער ונגינות שותי שכר
13 Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.
ואני תפלתי-לך יהוה עת רצון-- אלהים ברב-חסדך ענני באמת ישעך
14 Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.
הצילני מטיט ואל-אטבעה אנצלה משנאי וממעמקי מים
15 Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina.
אל-תשטפני שבלת מים-- ואל-תבלעני מצולה ואל-תאטר-עלי באר פיה
16 Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.
ענני יהוה כי-טוב חסדך כרב רחמיך פנה אלי
17 Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.
ואל-תסתר פניך מעבדך כי-צר-לי מהר ענני
18 Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana.
קרבה אל-נפשי גאלה למען איבי פדני
19 Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.
אתה ידעת--חרפתי ובשתי וכלמתי נגדך כל-צוררי
20 Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.
חרפה שברה לבי-- ואנושה ואקוה לנוד ואין ולמנחמים ולא מצאתי
21 Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.
ויתנו בברותי ראש ולצמאי ישקוני חמץ
22 Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko.
יהי-שלחנם לפניהם לפח ולשלומים למוקש
23 Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.
תחשכנה עיניהם מראות ומתניהם תמיד המעד
24 Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu.
שפך-עליהם זעמך וחרון אפך ישיגם
25 Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.
תהי-טירתם נשמה באהליהם אל-יהי ישב
26 Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.
כי-אתה אשר-הכית רדפו ואל-מכאוב חלליך יספרו
27 Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.
תנה-עון על-עונם ואל-יבאו בצדקתך
28 Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai.
ימחו מספר חיים ועם צדיקים אל-יכתבו
29 Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.
ואני עני וכואב ישועתך אלהים תשגבני
30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
אהללה שם-אלהים בשיר ואגדלנו בתודה
31 Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.
ותיטב ליהוה משור פר מקרן מפריס
32 Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!
ראו ענוים ישמחו דרשי אלהים ויחי לבבכם
33 Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.
כי-שמע אל-אביונים יהוה ואת-אסיריו לא בזה
34 Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,
יהללוהו שמים וארץ ימים וכל-רמש בם
35 gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,
כי אלהים יושיע ציון ויבנה ערי יהודה וישבו שם וירשוה
36 ’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.
וזרע עבדיו ינחלוה ואהבי שמו ישכנו-בה

< Zabura 69 >