< Zabura 65 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu
2 Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo.
3 Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu.
4 Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki.
5 Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa,
6 wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,
7 wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai.
8 Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.
9 Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara.
10 Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.
11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.
12 Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna.
13 Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki.