< Zabura 63 >
1 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.
A Psalm of David, when he was in the wilderness of Judah. O God, thou art my God; early will I seek thee: my soul thirsteth for thee, my flesh longeth for thee in a dry and thirsty land, where no water is;
2 Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
To see thy power and thy glory, so as I have seen thee in the sanctuary.
3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.
Because thy lovingkindness is better than life, my lips shall praise thee.
4 Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
Thus will I bless thee while I live: I will lift up my hands in thy name.
5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
My soul shall be satisfied as with marrow and fatness; and my mouth shall praise thee with joyful lips:
6 A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.
When I remember thee upon my bed, and meditate on thee in the night watches.
7 Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
Because thou hast been my help, therefore in the shadow of thy wings will I rejoice.
8 Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
My soul followeth hard after thee: thy right hand upholdeth me.
9 Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.
But those that seek my soul, to destroy it, shall go into the lower parts of the earth.
10 Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.
They shall fall by the sword: they shall be a portion for foxes.
11 Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.
But the king shall rejoice in God; every one that sweareth by him shall glory: but the mouth of them that speak lies shall be stopped.