< Zabura 62 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.
למנצח על ידותון מזמור לדוד אך אל אלהים דומיה נפשי ממנו ישועתי׃
2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
אך הוא צורי וישועתי משגבי לא אמוט רבה׃
3 Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?
עד אנה תהותתו על איש תרצחו כלכם כקיר נטוי גדר הדחויה׃
4 Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. (Sela)
אך משאתו יעצו להדיח ירצו כזב בפיו יברכו ובקרבם יקללו סלה׃
5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.
אך לאלהים דומי נפשי כי ממנו תקותי׃
6 Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
אך הוא צורי וישועתי משגבי לא אמוט׃
7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
על אלהים ישעי וכבודי צור עזי מחסי באלהים׃
8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. (Sela)
בטחו בו בכל עת עם שפכו לפניו לבבכם אלהים מחסה לנו סלה׃
9 Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.
אך הבל בני אדם כזב בני איש במאזנים לעלות המה מהבל יחד׃
10 Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.
אל תבטחו בעשק ובגזל אל תהבלו חיל כי ינוב אל תשיתו לב׃
11 Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,
אחת דבר אלהים שתים זו שמעתי כי עז לאלהים׃
12 kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”
ולך אדני חסד כי אתה תשלם לאיש כמעשהו׃

< Zabura 62 >