< Zabura 60 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!
For the Leader; upon Shushan Eduth; Michtam of David, to teach; when he strove with Aram-naharaim and with Aram-zobah, and Joab returned, and smote of Edom in the Valley of Salt twelve thousand. O God, Thou hast cast us off, Thou hast broken us down; Thou hast been angry; O restore us.
2 Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.
Thou hast made the land to shake, Thou hast cleft it; heal the breaches thereof; for it tottereth.
3 Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.
Thou hast made Thy people to see hard things; Thou hast made us to drink the wine of staggering.
4 Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka. (Sela)
Thou hast given a banner to them that fear Thee, that it may be displayed because of the truth. (Selah)
5 Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
That Thy beloved may be delivered, save with Thy right hand, and answer me.
6 Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.
God spoke in His holiness, that I would exult; that I would divide Shechem, and mete out the valley of Succoth.
7 Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina.
Gilead is mine, and Manasseh is mine; Ephraim also is the defence of my head; Judah is my sceptre.
8 Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”
Moab is my washpot; upon Edom do I cast my shoe; Philistia, cry aloud because of me!
9 Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?
Who will bring me into the fortified city? Who will lead me unto Edom?
10 Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?
Hast not Thou, O God, cast us off? And Thou goest not forth, O God, with our hosts.
11 Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.
Give us help against the adversary; for vain is the help of man.
12 Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.
Through God we shall do valiantly; for He it is that will tread down our adversaries.

< Zabura 60 >