< Zabura 6 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit. Ta Dawuda. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
2 Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
3 Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
4 Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
5 Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari? (Sheol )
6 Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.
7 Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
8 Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.
9 Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.
10 Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.