< Zabura 59 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
למנצח אל תשחת לדוד מכתם בשלח שאול וישמרו את הבית להמיתו הצילני מאיבי אלהי ממתקוממי תשגבני׃
2 Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.
הצילני מפעלי און ומאנשי דמים הושיעני׃
3 Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
כי הנה ארבו לנפשי יגורו עלי עזים לא פשעי ולא חטאתי יהוה׃
4 Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
בלי עון ירוצון ויכוננו עורה לקראתי וראה׃
5 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. (Sela)
ואתה יהוה אלהים צבאות אלהי ישראל הקיצה לפקד כל הגוים אל תחן כל בגדי און סלה׃
6 Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
ישובו לערב יהמו ככלב ויסובבו עיר׃
7 Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
הנה יביעון בפיהם חרבות בשפתותיהם כי מי שמע׃
8 Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.
ואתה יהוה תשחק למו תלעג לכל גוים׃
9 Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,
עזו אליך אשמרה כי אלהים משגבי׃
10 Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
אלהי חסדו יקדמני אלהים יראני בשררי׃
11 Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su.
אל תהרגם פן ישכחו עמי הניעמו בחילך והורידמו מגננו אדני׃
12 Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
חטאת פימו דבר שפתימו וילכדו בגאונם ומאלה ומכחש יספרו׃
13 ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. (Sela)
כלה בחמה כלה ואינמו וידעו כי אלהים משל ביעקב לאפסי הארץ סלה׃
14 Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
וישובו לערב יהמו ככלב ויסובבו עיר׃
15 Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.
המה ינועון לאכל אם לא ישבעו וילינו׃
16 Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.
ואני אשיר עזך וארנן לבקר חסדך כי היית משגב לי ומנוס ביום צר לי׃
17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.
עזי אליך אזמרה כי אלהים משגבי אלהי חסדי׃

< Zabura 59 >